Majalisar Wakilai ta dakatar da zaman data shirya akan kudurorin sake fasalin Harajin biyo bayan matsin lamba daga gwamnonin jihohin Arewa 19.
An dakatar da muhawarar da aka shirya yi a wata takarda mai dauke da sa hannun magatakardar Majalisar Dr Yahaya Danzaria bayan da ‘yan majalisar arewa 73 suka ki amincewa da kudirin.
Wadanda suka ki amincewa da kudirin sun hada da ‘yan majalisar wakilai 48 daga yankin Arewa maso Gabas, ‘yan majalisar tarayya 24 daga Kano da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, mai wakiltar Sokoto ta Kudu.
Sanarwar tace “Shugaban majalisar ya umurce ni da in sanar da daukacin ‘yan majalisar cewa an dage zama na musamman da aka shirya gudanarwa a ranar Talata 3 ga watan Disamba, 2024, domin tattauna duk wasu kudirin gyara harajin zuwa wani lokaci nan gaba.
“Hakan ya biyo bayan buƙatar ƙarin tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki. Za a sanar da sabon kwanan wata da wurin zama a lokacin da ya dace. Mun yi nadamar duk wani rashin jin daɗi da wannan zai iya haifarwa kuma mun yaba da fahimtar ku.” a cewar sanarwar.
DAILY POST Hausa ta rawaito cewa a ranar 3 ga Satumba, 2024 Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Majalisar Dokoki ta kasa wasu kudurori guda huɗu na sake fasalin haraji don tantance su biyo bayan shawarwarin Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kuɗi da Harajin karkashin jagorancin Taiwo Oyedele.
Saidai kudurorin hudu su haifar da cecekuce musamman tsakanin masu ruwa da tsaki a yankin Arewacin kasarnan.
Majalisar Wakilai ta dakatar da zama akan kudurin gyaran haraji