Majalisar wakilai ta gabatar da wasu kudirori guda biyu domin magance matsalolin da ake samu kan jinkirin gabatar da kasafin kudin da shugaban kasa da gwamnoni ke yi tare da takaita adadin karin kasafin da za a amince da shi don magance gibin kudade a cikin kasafin shekara.
Kudirorin doka guda biyu suna gaban kwamitin wucin gadi kan sake duba akan kundin tsarin mulki na majalisar karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu.
Daya daga cikin kudurorin mai suna, “Kudirin dokar da za ta yi wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya kwaskwarima, 1999 domin takaita wa’adin gabatar da kasafin kudi a gaban majalisun dokoki na kasa da Jihohi.”
Kudirin ya samu ne ta hannun dan majalisa Mansur Manu Soro da kuma dan majalisar wakilai Emeka Martins Chinedu ya bukaci a bayyana lokacin da za a gabatar da kasafin kasa da na Jihohi a gaban Majalisar Kasa da Majalisun Jihohi don magance mummunan tasirin jinkirin da ake samu daga shugabanni wajen gabatar da kudurin.
Hakazalika, wani kudirin doka wanda dan majalisa Mansur Manu Soro da dan majalisa Adamu suka dauki nauyinsa ya nemi a takaita adadin karin kasafin kudi na kasa zuwa sau daya kawai a kowace shekara.
Majalisar wakilai ta gabatar da kudirorin gyaran matsalolin kasafin kudi