Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya zargi wasu mutane da rashin son kawo karshen ayyukan ta’addancin Boko Haram saboda suna cin gajiyar lamarin.
Zulum, wanda ya bayyana hakan a wata hira da BBC Hausa, ya koka da yadda wasu mutane da ya ce suna samun riba daga rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas da tafkin Chad, ke hana a kawo karshen yaki da ‘yan ta’addan.
“Wasu ba sa son wannan rashin tsaro ya kare saboda ba za su ji dadi da hakan ba,” inji shi.
Gwamnan, wanda ya bayyana cewa an samu ci gaba a yaki da ‘yan ta’addan, ya koka da cewa yanzu ‘yan Boko Haram sun fara dawowa yankin bayan an kore su daga Chad.
Ya yi kira ga mutane su hada kai tare da goyon bayan jami’an tsaro don magance matsalar Boko Haram.
Sai dai gwamnan bai bayyana takamaiman wadanda ke cin gajiyar rashin tsaron yankin ba.
Masu cin gajiyar fadan Boko Haram ba sa so a daina – Gwamna Zulum