in

Masu sukar Tinubu makiyan Najeriya ne – Umahi

Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya ce wadanda ke sukar gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa suna yin hakan ne saboda hassada, kuma ya bayyana su a matsayin masu adawa daci gaban Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake tabbatar da cewa gyare-gyaren da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a halin yanzu za su gyara tattalin arzikin kasa cikin lokaci ba mai tsawo ba.

Umahi ya yi wannan bayani a gefen zaman sauraron bayanai na kwamitin ayyuka na Majalisar Dattawa da aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a.

Ya jaddada cewa shugabannin sassa daban-daban na tattalin arziki sun fahimci muhimmancin wannan gyara kuma suna aiki tare domin cimma nasararsa.

Da yake magana kan cece-kuce game da aikin hanyar tekun Legas zuwa Calabar, Umahi ya ce sukar da ake yi “ta samo asali ne daga hassada da kishi.”

“Mai Girma Shugaban Kasa yana da wannan burin kyautata Najeriya tun shekaru 25 da suka gabata lokacin da yake gwamna, kuma yanzu Allah Ya ba shi dama ya yi wa ƙasar hidima tare da cika burinsa, don haka babu yadda za a yi ya kaucewa yin aiki tukuru,” in ji shi.

“Abin da ya yi na yarda da ya ci gaba da dukkan ayyukan wanda ya gabace shi abu ne mai wuya sosai a ga wani shugaban kasa ya yi,” ya ƙara da cewa.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu
yana sauya alkiblar Najeriya zuwa hanya mai kyau, tareda cewa masu suka basuyi tunanin zai iya cimma hakan cikin ɗan
takaitaccen lokaci tun bayan hawa mulki ba.

Yace, “idan mutane sun daina wannan halin zargi kuma suka fahimci mahimmancin aikin hanyar tekun sosai, za su gane cewa wannan aiki ginshiƙi ne ga ci gaban kowace jiha a wannan ƙasa.”

Masu sukar Tinubu makiyan Najeriya ne – Umahi

Activate alert systems on COVID-like symptoms – FG advises tertiary hospitals

Police arrest suspected gunman, recover AK47 rifle