in

Matar shugaban Miyetti Allah Kyautal Hore ta roki Tinubu ya sa hannu a saki mijinta

Iyalan Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Kyautal Hore, Alhaji Bello Boɗejo sun bukaci Shugaba Tinubu Tinubu ya sa baki sojoji su sako shi.

Matarsa, Hajiya Hauwa Bello Boɗejo ta roƙi hukumomi da kungiyoyin ƙasashen duniya da kungiyoyin fararen hula da masu faɗa a ji a Nijeriya da su sa baki cikin lamarin mijin nata.

Hajiya Hauwa ta ce tsarewar da aka yi mijinta ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, ya jefa shi da su duka cikin tashin hankali.

Ta ce rashin lafiyar da yake fama da ita ta ƙara tsananta, don haka ta roki Tinubu ya sanya baki a lamarin domin sojoji su sako mijin nata.

Idan za’a iya tunawa dai sojoji daga Runduna ta 177 da ke Keffi a Jihar Nasarawa ne suka yi dirar mikiya a gidan Bello Boɗejo suka yi awon gaba da shi, daga bisani suka damƙa shi ga Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA).

Matar shugaban Miyetti Allah Kyautal Hore ta roki Tinubu ya sa hannu a saki mijinta

NEMA ta rabawa wadanda ambaliya ta shafa a Zamfara tallafi

Gwamnan Ebonyi ya baiwa ma’aikatan jihar N150,000 don bikin kirsimeti