Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) reshen Kano ya ce ya karɓi korafe-korafe 1,600 da suka shafi cin zarafin mata da yara (SGBV) a wannan shekara, wanda ya nuna ƙaruwa daga kashi biyar zuwa shida cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2023.
Kwamandan hukumar a jihar Kano, Abdullahi Shehu, ne ya bayyana hakan yayin taron bita na kwana ɗaya da ƙaddamar da dandamalin rahoton cin zarafin mata na Women Radio wanda ƙungiyar Voices Beyond Silence Initiative (VOBSI) ta shirya, tare da haɗin gwiwar Cibiyar nazarin jinsi ta Jami’ar Bayero, Kano.
Shehu ya bayyana cewa cin zarafin jinsi ya yi kamari a Kano, musamman ga mata da yara a gidajen aure. Ya ce, “Baya ga fyade, akwai wasu nau’o’in cin zarafi kamar rashin kulawa da hakkokin iyali da ke jefa mata da yara cikin damuwa ta da kan shafi lafiyar kwawalwarsu”
Ya kara da cewa “Ofishin mu ya karɓi korafe-korafe 1,600 a shekarar 2024, wanda ya nuna ƙaruwa daga kashi biyar zuwa shida idan aka kwatanta da adadin da muka samu a shekarar 2023.”
Mun samu korafin cin zarafin mata 1,600 a 2024 – NHRC