Mutum 3 ne suka rasa ransu a Kano a ibtila’in gobara a cikin watan Nuwamba.
Wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara na Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya fitar a yammacin Talata, ta ce wasu 3 kuma sun jikkata, yayin da aka yi nasarar kubutar da mutum 4.
An kuma yi asarar dukiya ta Naira miliyan 132,450, an tserar da dukiya ta sama da Naira miliyan 310,600, cikin kiran waya 43 da hukumar ta samu.
Sanarwar ta yi kira ga alumma da su dinga tuki cikin nutsuwa da kuma gujewa gudun wuce sa’a.
Mutane 3 ne suka rasa ransu a ibtila’in gobara a Kano – Hukumar Kashe Gobara