Tsohon shugaban kwamitin kudi na majalisar wakilai, Faruk Lawan, ya bayyana hukuncin da aka yanke masa na zaman gidan yari na shekaru bakwai a matsayin ƙaddara.
Da yake magana a ranar Asabar yayin ziyarar da ya kai mazabar Shanono/Bagwai tare da magoya bayan siyasa, Faruk Lawan ya ce, “Yau, na kara zama mutum na gari, kuma na gode wa Allah a kan komai. Ziyarar ba ta siyasa ba ce, sai dai kawai don yin ta’aziyya, jajantawa ga masu rashin lafiya, da kuma girmama iyayenmu da shugabannin gargajiya.”
Faruk, wanda ya sa kayan rawani na Kwankwasiyya mai launin fari da ja.
“A halin yanzu, ina siyasa ne, amma ba na goyon bayan kowa,” inji shi.
Hakimin Bagwai Alhaji Nura Shehu Ahmad, Magajin Rafi na Kano, ne ya tarbe shi a karakara hukumar bakwai, ya kuma bayyana
zaman gidan yarin Faruk Lawan a matsayin “albarka ce a boye” gareshi da magoya bayansa.
Ya ce, “Yau, da yawa daga cikinmu da suka taba kasancewa abokan hamayyarka sun zama magoya bayanka na hakika,” a cewarsa.
Ya ce hakan ya biyo bayan sun fahimci wanene Faruk Lawan da yadda yake kishin al’ummarsa.
Hakimin ya bayyana cewa, “Ko da lokacin da Faruk Lawan yake a gidan yari, ya ci gaba da kula da mu a fannoni daban-daban na rayuwa. Ya tallafa wa mabukata, ya tambayi halin da kowa ke ciki, kuma ya aika saƙonni zuwa gare mu da dama. Mun gode maka sosai kuma mun gode.”
A karamar hukumar Shanono, hakimin Shanono, Ibrahim Sani Gaya Uban Doman Kano, ne ya tarbe Faruk Lawan, wanda ya yi tsokaci kan kyawawan halayensa tare da karfafa masa gwiwa ya dauki wannan gwajin a matsayin jarrabawa ga imaninsa.
Wani babban jigo a jam’iyyar NNPP, Saidu Sarkin Ya, wanda ke cikin tawagar, ya bayyana cewa, “Kowane lokaci, a duk inda ya ke, Faruk Lawan zai iya cin zabe duk da ba ya nan. Muna roƙon gwamnatin tarayya ta yi masa afuwa tare da cire sunansa daga cikin masu laifi domin ya ci gaba da siyasa.”
Faruk Lawan ya samu rakiyar shugabannin ƙananan hukumomin Shanono da Bagwai, Alhaji Habu Barau da Alhaji Bello Abdullahi Kiyawa, tare da masu rike da mukaman siyasa daga Kano, shugabannin jam’iyyar NNPP, magoya bayan jam’iyyun APC da PDP, da ɗaruruwan magoya.
DAILY POST ta ruwaito cewa kotu ta yankewa tsohon shugaban kwamitin bincike na majalisar wakilai kan tsarin tallafin man fetur, Faruk Lawan, hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai saboda karɓar cin hancin $3m daga hamshakin attajirin mai, Femi Otedola.
Mai shari’a Angela Otaluka ta babbar botun FCT da ke Apo ta same shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume uku da ICPC ta shigar, kuma ta umarce shi da ya mayar da $500,000 ga gwamnatin tarayya.
Na kara zama mutum na kwarai bayan zaman gidan yari na shekaru 7 – Faruk Lawan