Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da mataimakiyar Sufeto ta Kwastam (Pilot) Olanike Nafisat Balogun ta zama mace ta farko da ta tukawa hukumar jirgi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta Kwastam Abdullahi Maiwada ya fitar, ya ce Balogun haifaffiyar garin Kaduna ce kuma ta shiga aikin kwastam a shekarar 2002.
Balogun tayi diploma a kan fannin Ticket da Cabin Services, da digiri na biyu a fannin Public Administration daga Jami’ar Ahmadu Bello, kafin daga bisani ta samu takardar shedar tukin jirgi a makarantar Flying Academy da ke Miami a jihar Florida, wadda Hukumar kwastam ta dauki nauyinta.
Ta jaddada nasarar da ta samu a matsayin abin zaburarwa ga mata da suke da burin tukin jirgi.
Nafisat Balogun ta zama mace ta farko da ta tukawa hukumar jirgi