Hukumar hana safarar mutane ta kasa NAPTIP ta dakile yunkurin wasu mutane 10 da suka yi kokarin tsallakawa kasashen ketare daga jihar kano domin ci rani.
Mutanen sun hada da mata shida da maza hudu ‘yan asalin jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa sun karbi rahoton ne daga rundunar yansandan Jihar kano a ranar bakwai ga watan disamban da muke ciki.
Mai magana da yawun hukumar reshen jahar kano malam Aliyu Abba Kalli ya ce mutanen suna kokarin tsallakawa kasar Libiya da kuma Italiya ta barauniyat hanya.
Aliyu Kalli yaja hankalin mutane wadan da suke da niyyar tafiya kasashen waje domin sana’a ko aiki su yi kokarin tafiya ta hukumar data dace.
NAPTIP ta kama mutane goma da suka yi kokarin tsallakawa ketare ta barauniyar hanya