Netflix ta bayyana cewa labaran da ke yawo game da ficewar kamfanin daga Najeriya ba gaskiya bane.
Kamfanin ya tabbatar da cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa a Najeriya.
Sun bayanna hakan ne, a cikin wata sanarwa da ta aike wa TechCabal.
A yayin da ta watsi da rade-radin, kamfanin ya bayyana cewa zai ci gaba da zuba jari a cikin labarun Najeriya don faranta wa masu kallo rai.
“Ba za mu bar Najeriya ba. Za mu ci gaba da zuba jari a cikin labarun kasar don jin daɗin membobinmu.”
DAILY POST Hausa, sun rawaito cewa Netflix, wanda ya shiga kasuwar Najeriya a 2016, ya haɓaka shirye-shiryen gida da dama zuwa ga masu kallo na duniya.
Netflix ta musanta rade-radin ficewa daga Najeriya