in

NOA za ta fassara kudurin dokar haraji zuwa harsuna 36

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta ce tana fassara sabuwar ƙudirin dokar haraji zuwa harsuna sama da 36 na kasar nan domin warware kuskuren fahimta game da dokar.

Shugaban Hukumar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka yi domin wayar da kan jama’a game da dokar harajin.

Inuwa Yusuf Kobi, daraktan bincike da kididdiga na NOA, shine ya wakilci shugaban hukumar a wajen taron, ya ce fahimtar doka zai bai wa mutane damar yanke hukunci mai kyau a kanta.

“An samu kuskuren fahimta da dama game da dokar gyaran haraji a cikin jama’a, kuma abin takaici, masu yin sharhi mara kyau game da sabbin dokar da yawa daga cikinsu ba su san cikakkun bayanai da fa’idodin da ke cikinsa ba,” in ji shi.

Ya ce hukumar ta yi haɗin gwiwa da shugabannin addini da gargajiya wajen wayar da kai domin warware kuskuren fahimta dake tattare da dokar.

“Da yawa sun fahimci cewa an sanya siyasa cikin batun, duk da amfanin da dokar ke dashi ga al’umma,” in ji shi.

Ya ce dokar gyaran haraji za ta magance matsalar yawan haraji da kuma kawo sassauci ga kasuwancin da ke da jari ƙasa da Naira miliyan 50.

NOA za ta fassara kudurin dokar haraji zuwa harsuna 36

Reps seek increase in DIA budgetary provision

NPFL: Akwa United appoint Uko interim technical adviser