A ranar Litinin ne sojojin Najeriya su ka gudanar da wani bikin sauke tuta da daga sabuwar tuta a Hedkwatar Soja yayin da Janar Olufemi Oluyede, ya karɓi ragamar shugabancin Sojojin Najeriya.
An naɗa Janar Oluyede ne a matsayin mukaddashin shugaba daga Shugaba Bola Tinubu a ranar 30 ga Oktoba, bayan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya (CDS), Christopher Musa, ne ya mika wa Jamar Oluyede alamar kama ofis a ranar 1 ga Nuwamba, kamar yadda dokar rundunar sojojin Najeriya ta tsara.
Bikin sauke da daga sabuwar tutar ya nuna cewa Janar Oluyede ya fara wa’adinsa, bayan majalisar dattijai da ta Wakilai sun tabbatar da naɗinsa.
Kafin wannan naɗi, Janar Oluyede ya kasance kwamandan runduna ta 56 ta Infantry Corps na Sojojin Najeriya, wanda ke Jaji, Kaduna.
Janar Oluyede mai shekara 56 da Laftanal Janar Lagbaja sun kasance abokan karatu kuma mambobi na karo na 39 na Kwalejin Tsaron Najeriya (NDA).
Oluyede ya shiga ofis a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na 24