in

Ooni na Ife ya ziyarci tsohon shugaban kasa Buhari a Daura

Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya ziyarci tsohon Shugaban Kasan, Muhammadu Buhari a Daura, Jihar Katsina, a ranar Laraba.

Wannan ziyarar ta kasance cikin wani ziyara na girmamawa, wanda Ahmad Bashir, tsohon mai ba da shawara na Buhari, ya bayyana ta cikin hotuna daya wallafa a shafin X.com.

Kafin Ooni yabar garin, ya ziyarci Fadar Sarki a Daura tare da Buhari.

Bashir ya rubuta a cikin bayaninsa cewa, “A yau, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi (Ọjájá II), ya ziyarci Daura tare da tawagarsa don ganin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

“Kafin barin Daura, tsohon shugaban ya jagoranci Ooni da tawagarsa zuwa Fadar Sarkin Daura.”

Ooni na Ife ya ziyarci tsohon shugaban kasa Buhari a Daura

UCL: Leading top scorers after this week’s matches

Nigerian man jailed for defrauding American of $115,000 in Bitcoin scam