A yau, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya ziyarci Asibitin Koyarwar Kashi na Ƙasa da ke Enugu, bayan wani mummunan labari na fashewar iskar gas da ya faru a kwanakin baya a gidan ɗaya daga cikin mambobin “Obidient” da ke amfani da @Uptownoflagos a shafinsa na sada zumunta.
Wannan hatsarin ya jawo wa ‘yan uwansa uku munanan raunin ƙonewar fata na mataki na uku (third-degree burns).
Obi ya bayyana cewa ya je don bayar da goyon baya da addu’o’i ga iyalan yayin wannan mawuyacin lokaci.
Ya ce, “Wannan mummunan al’amari ba dadi. Addu’ata da ta’aziyyata na tare da waɗanda abin ya shafa, iyalansu, da duk waɗanda ke fama da irin wannan matsala a faɗin ƙasar nan.
Ina ci gaba da addu’a don samun sauƙinsu gabaki ɗaya, tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki ya basu lafiya, ƙarfi, da kwanciyar hankali.”
Obi ya kuma yi kira ga al’umma da su haɗa kai wajen gina ƙasa mai cike da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da wadatar abubuwan more rayuwa.
Ya ce, “Yayin da muke aiki don gina ƙasa inda tsaro, kiwon lafiya, da abubuwan more rayuwa suke zama fifiko, mu ci gaba da kasancewa masu haɗin kai da goyon bayan juna.”
Peter Obi ya taimaka wa iyalan da lamarin fashewar gas ya shafa