in

Sarki Sanusi ya dakatar da dagaci

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya dakatar da dagacin garin dogon kawo dake karamar hukumar dogowa Malam Kailani Yusuf bisa zargir karbar kudi naira dubu dari shida dayayi a hannun wani mutum Mai suna Alhaji Damuna Sule kan wata gona daya siyar masa.

Tuni Mai martaba Sarki yayi umarnin dagacin daya dawo musu da kudinsu kuma sarki ya dakatar dashi har sai angama bicike.

A wani labarin kuma Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya yabawa ƙungiyar malaman sakandare ta kasa reshen jihar Kano karkashin jagorancin Hajiya Uwani Balarabe bisa kokarinsu na ciyar da ilimin gaba a jihar nan dama kasa baki daya.

A nata jawabin shugabar ƙungiyar Hajiya Uwani Balarabe tace sunzo fadar Mai martaba sarkin ne don Neman shawarwarinsa da kuma sanar dashi taronsu da zasu yi akan habaka hankokin ilimi.

Sarkin ya kuma Karbi bakoncin tsoffin daliban makarantar rumfa aji na tamanin da bakwai karkashin jagorancin shugaban daliban Malam koguna.

Sarki Sanusi ya dakatar da dagaci

Circular Road: Oyo govt begins re-verification of houses affected land acquisition

Mun samu korafin cin zarafin mata 1,600 a 2024 – NHRC