Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Mista Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin mai rikon mukamin Akanta Janar kasa (AGF).
An sanar da wannan nadin ne bayan fara hutun ritaya da AGF mai rike da mukamin a yanzu, Dr. Oluwatoyin Sakirat Madein tayi
Wannan matakin yana nufin tabbatar da canji mai sauki a Ofishin Accountant General na Tarayya (OAGF) yayin ci gaba da tsarin canje-canjen manufofin kudi na gwamnatin wannan lokaci.
Ogunjimi, wanda ya kasance ma’aikacin gwamnati mai kwarewar sama da shekaru 30 a fannin gudanar da kudi, ya rike manyan mukamai ciki har da Daraktan Kudi a mai’katar kudi da Ma’aikatar Harkokin Waje.
Ogunjimi na da digirin farko a fannin Lissafi da kuma digirin na biyu Master’s a fannin Kudi da Lissafi.
Shugaba Tinubu ya nuna yakinin cewa kwarewar Ogunjimi za ta kara karfafa ayyukan tattalin arziki a Najeriya.
Haka kuma, ya yi godiya ga AGF mai ritaya, Dr. Madein, saboda sadaukar da ita ga aikin gwamnati.
Dr. Madein, wacce za ta tafi ritaya a ranar 7 ga Maris, 2025, ta kai shekarun ritaya da aka tanada a cikin aikin gwamnati.
Shugaba Tinubu ya nada sabon akanta janar