in

Shugaba Tinubu ya yi alkawarin kara gina ingantattun kayan more rayuwa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za a ci gaba da aiwatar da ayyukan bunkasa ababen more rayuwa da ke da muhimmanci ga al’umma, musamman hanyoyin mota a fadin kasar.

Shugaban ya bayar da wannan tabbaci ne ta bakin karamin Ministan ayyuka, Mohammed Bello Goronyo, yayin wata ziyara da ya kai wa gwamnan nihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa ci gaba da aikin gina babbar hanyar mota daga Sokoto zuwa Badagry wata shaida ce ta kudirin Shugaba Tinubu na aiwatar da ayyukan ci gaban Najeriya.

Ministan ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai shirin yi wa al’umma hidima tare da mayar da hankali wajen cimma manufofin da ya yi alkawari.

Ya ce babbar hanyar daga Illela a jihar Sokoto zuwa Badagry a jihar Lagos za ta bude hanyoyin kasuwanci masu yawa, rage matsalar tsaro, tare da rage tsawon lokacin tafiya.

Ya kara da cewa ziyararsa zuwa jihar Kebbi wani bangare ne na zagayen aiki, tare da kaddamar da wata gada da aka gyara a garin Alawasa da ke kan hanyar Sokoto zuwa Birnin Kebbi, wadda ruwan sama ya lalata damunar da ta wuce, wacce hukumar FERMA ta gyara.

A bayaninsa, gwamna Nasir Idris ya yaba da ayyukan da FERMA ke yi a jihar ta fuskar gyaran hanyoyi da kula da su.

Gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu saboda saka jihar Kebbi cikin aikin gina babbar hanyar daga Illela a jihar Sokoto zuwa Badagry a Jihar Lagos, wanda zai kawo ci gaban tattalin arziki ga al’ummar jihar Kebbi.

Shugaba Tinubu ya yi alkawarin kara gina ingantattun kayan more rayuwa

Transfer: Sparta Prague sign Nigerian defender, Emmanuel

Era of bank robbery long gone – IGP