Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tarbi Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier a Fadar Aso Rock, Abuja, da safiyar Laraba.
Steinmeier, wanda ya isa Abuja da yammacin Talata, ya hadu da Shugaban kasa a Farfajiyar Fadar da misalin karfe 11:06 na safe.
Ya zo tare da wata tawaga ta shugabannin kamfanoni da manyan mambobin kwamitin gudanarwa na wasu daga cikin manyan kamfanonin Jamus da su ka yi shura a fannonin fasahar sadarwa (IT), fasahar zamani, da makamashi.
An tarbi shugaban da taken kasar Jamus da kuma na Najeriya.
Daga baya, Tinubu ya jagoranci Steinmeier zuwa ofishinsa domin gudanar da tattaunawar sirri.
A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Jamus ya fitar a ranar Litinin, an ce Steinmeier zai gana da Tinubu da kuma Shugaban Hukumar Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Dr. Alieu Touray.
Shugaban Jamus, Steinmeier ya kawo ziyarar aiki Najeriya