Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) za su gudanar da taro a ranar Lahadi a Abuja, inda ake sa ran za su tattauna batun kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso da su ka fice daga cikin kungiyar.
Tuno ƙasashen uku su ka tabbatar da ficecwarsu daga kungiyar watanni 11 da gabata, kuma wa’adin shekara guda da ƙa’idar ECOWAS ta tanada ga kowace ƙasa da ke son ficewa daga ƙungiyar zai cika a watan Janairu mai zuwa.
A makon da ya gabata, shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Tinubu, ya bayyana wa shugaban Jamus, Frank-Walter Steinmeier, cewa muradun al’ummomin Burkina Faso, Mali, da Nijar na daga cikin manyan abubuwan da shugabannin ECOWAS ke mayar da hankali a kai.
Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa zai ci gaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya da hikima domin ganin ƙasashen yankin Sahel sun dawo cikin ƙungiyar, tare da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a yankin.
Sauran batutuwan da suka shafi haɗin kai, tsaro, da ci gaban tattalin arzikin yankin na cikin ajandar da ake sa ran ECOWAS za ta mayar da hankali a kai.
Shugabannin ECOWAS za su gana a Abuja