Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da safarar makamai yayin wani samamen kwanton-bauna a garin Bokkos, jihar Filato.
Majiyoyin sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa wadanda ake zargin, wadanda aka bayyana sunayensu da Mista Kenneth Mayas mai shekara 31 da Mista Bulus Yilfo mai shekara 60, an kama su a wani maboya a Otel ɗin White House a ranar Juma’a yayin da suke ƙoƙarin siyan bindigar AK-47 akan kudi Naira miliyan 1.45.
Duk mutanen biyu sun fito daga yankin Forop da ke laramar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.
Yayin samamen, sojojin sun kwato kuɗi har Naira miliyan 1.45 daga hannun waɗanda ake zargin, waɗanda ake zaton suna cikin wata babbar ƙungiyar aikata laifi.
Majiyoyin sun bayyana cewa waɗanda aka kama tare da kuɗin da aka kwato suna hannun jami’ai don bincike, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mambobin ƙungiyar.
Sojoji sun kama masu safarar makamai ana tsaka da cinikin AK47