Tsofaffin sojojin Najeriya da suka yi ritaya a yau, Alhamis sun gudanar da zanga-zanga a gaban Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ke Abuja, suna neman a biya su hakkokinsu da suka shafi fansho da sauran alawus-alawus da ba a cika ba.
Tsofaffin sojojin sun zargi Gwamnatin Tarayya da rashin biyan su karin albashi na kashi 20% zuwa 28% daga Janairu zuwa Nuwamba 2024.
Daga cikin bukatunsu har da biyan su kudaden tallafi na watan Oktoba 2023 zuwa Nuwamba 2024, karin N32,000 a kan fansho, kudin Security Debarment Allowance, da kuma mayar da kudaden da aka cire daga fanshon sojojin da aka sauke saboda matsalolin lafiya, tare da sauran bukatu.
Sun kawo tabarmai, kujeru, da rumfuna zuwa wurin zanga-zangar.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Kanal Innocent Azubuike (ritaya), ya koka kan halin da tsofaffin sojojin ke ciki, yana mai cewa rashin biyan hakkokinsu ya jefa su cikin mawuyacin hali.
Ya bayyana cewa, duk da alkawarin da aka yi na biyan hakkokin su a watan Nuwamba, an shaida musu cewa ba za a iya biyan ba saboda rashin isassun kudade.
Azubuike ya ce, “An fada mana cewa an samu amincewa kan biyan hakkokinmu, abinda ya rage kawai shi ne a samu kudin biyan.
“An bukaci mu yi hakuri tare da tabbacin cewa za a biya mu hakkokinmu da suka jima ana binmu a watan Nuwamba. Amma ga shi Nuwamba ya wuce, ba tare da wani alamun lokacin da za a biya ba, saboda al’amarin yana hannun Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, ba Ma’aikatar Tsaro ba.”
Sojojin da suka yi ritaya sun rufe ma’aikatar kudi a Abuja