Sojojin Rundunar 6 ta Sojojin Najeriya/Sashe na 3 na Aikin Whirl Stroke sun kubutar da mutane uku da akayi garkuwa dasu a kauyen Manzala, karamar hukumar Yorro a Jihar Taraba.
Bayan samun rahoton gaggawa kan ayyukan ‘yan bindiga a wannan yankin a ranar 13 ga Disamba, 2024, sojojin sun dauki mataki nan take inda suka isa wurin. Bayan fafatawa da masu garkuwa, sun samu nasarar kubutar da mutane uku.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojoji ta 6, Olubodunde Oni, ya ce wadanda aka kubutar din sun koma ga iyalansu lafiya.
Daga nan, sojojin sun gudanar da sintirin yaki a yankunan tsaunuka tare da gano wuraren da ake samun barazana a kananan hukumomin Ardo-Kola da Yorro, domin kara tabbatar da tsaro da doka.
Haka kuma, a ranar 12 ga Disamba, 2024, yayin da sojojin ke sintiri a kan titin Takum zuwa Katsina Ala, sun tarar da wani harin fashi da akeyi a kusa da Kasuwan Shanu da ke garin Takum.
Dabarun gaggawa sun kai ga cafke wani da ake zargi da fashi da makami mai suna Emmanuel Thomas Oryiman, wanda aka samu da bindiga da aka kera a gida da harsasai biyu na 9mm.
Kwamandan Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya bayyana cewa nasarorin da aka samu karkashin Aikin GOLDEN PEACE sun yi nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Taraba da wasu sassan Jihar Benue.
Wannan mataki yana nufin hana ‘yan ta’adda damar aikata laifi tare da karfafa tsaro a cikin yankin da rundunar ke kula da shi.
Kwamandan ya yabawa jarumtaka da kwarewa, da saurin daukar matakin da sojojin suka nuna, sannan ya tabbatarwa da al’umma cewa Sojojin Najeriya za su ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma, ya bukaci mazauna yankin su ci gaba da baiwa sojoji goyon baya ta hanyar bayar da sahihin bayani domin taimakawa wajen yaki da miyagun mutane.
Sojojin sun kubutar da mutane uku da akayi garkuwa dasu a Taraba