in

Tinubu ya kudunduno harajin gado cikin kudirin dokar haraji ta 2025 – Farfesa Dandago

Tsohon Kwamishinan Kudi na jihar Kano, Farfesa Kabiru Isa Dandago ya zargi gwamnatin tarayya da bullo da harajin gado cikin kudirin dokar haraji da ake takaddama a kai.

Kudurin dake gaban majalisar dattawa yanzu haka na cigaba da shan suka daga manyan Arewa bayan yi masa karatu na biyu, sai dai kafin yanzu babu wani masani da ya gano batun harajin gadon da Farfesa Dandago yace an boye shi cikin dokar.

Farfesan ya shaidawa DAILY POST HAUSA cewa babi na biyu sashi na daga, saki layi na uku, yayi bayani kan kudin iyali da za a cire gado a ciki kafin a raba.

“Wannan ba shine karon farko da aka taba bijiro da harajin gado ba a Najeriya, tsohon sbugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gwada yin haka a 1979 sai dai marigayi Janar Sani Abacha ya soke dokar lokacin mulkinsa bayan malaman addinin muslunci da na kirista sun kalubalance ta” .

Sidarar ta tanadi cire haraji cikin kudin gadon da Iyali zasu samu kafin a raba, sai dai bata fayyace ko nawa ne za a cire ba, amma Farfesa Dandago yace;

“Tunda ba a fadi ko nawa za a cire ba to za a yi wa wannan kallon kowane irin haraji.”

“Daga Naira miliyan biyu da dubu 200, za a cire kashi 15 cikin dari a matsayin haraji, har zuwa kashi 60% ga kudin da ya haura Naira miliyan 190, wato inda zai kama Naira miliyan 113,530.00 a matsayin haraji, yayin da magada za a barsu da ragowar Naira miliyan 76,470.00”

Farfesan yace idan batun ya tabbata, bashakka ya sabawa koyarwar addinin musulunci, saboda Allah ne da kansa ya raba gado, bai kuma ce a baiwa hukuma ko kobo ba.

Wasu rahotanni na cewa shugaban kasar ka iya janye kudurin kowane lokaci daga yanzu bayan matsin lamba daga masu adawa da shi, da suka hada gwamanoni da yan siyasa da malamai da kuma sarakunan arewacin Najeriya.

Tinubu ya kudunduno harajin gado cikin kudirin dokar haraji ta 2025 – Farfesa Dandago

Release Nnamdi Kanu to address South-East crisis – Igbo group tells Tinubu

Zamfara Chief Judge demands financial autonomy for judiciary