Bayan shekara guda da kai harin bam kauyen Tudun biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, har yanzu babu wanda aka hukunta kan batun.
Ranar 3 ga watan Nuwamban 2023, wani jirgin ya jefa bam bisa kuskure kan masu maulidi a kauyen, abinda yayi sanadiyyar mutane masu yawa.
Tun a wancan lokaci, gwamnati ta yi alkawari na inganta rayuwar mutanen garin tare da sake gina garin, ta kuma ci alwashin gabatar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru tare da hukunta wadanda aka samu sakaci.
Sai dai har yau babu wanda aka tuhuma da sakaci wajen faruwar hadarin, al’ummar garin dai sun ce da yawa daga cikin alkawuran da ka yi musu ba a cika ba, yayin da wasu kuma har yanzu ba a kammala ba, kamar aikin baban titin dake shiga garin.
Wasu mazauna garin da suka tattauna da manema labarai sun gode wa gwaman jihar kan gina asibiti da cibiyar koyan sana’a da kuma sabbin gidaje da gwamantin ke yi yanzu haka.
A jawabinsa yayin ziyarar da ya kai garin, Gwamnan jihar Malam Uba Sani yace “har yanzu muna bin gwamnatin tarayya domin ganin an zakulo wadanda suka yi wannan abu kuma an hukunta su, ko nan da shekara nawa ne, zamu cigaba da bibiya”.
Gwamnan ya ce gwamnati za ta sake baiwa wadanda aka karbi gonakinsu domin gina gidaje wasu sabbin gonakin duk da cewa an biya su diyya a baya.
An dai rabawa al`ummar garin tallafin takin zamani da sauran kayan abinci da suka hada shinkafa da masara.
Tudun biri : Zamu tabbatar an hukunta masu laifi – Uba Sani