in

Turawa za su taimakawa mazauna Sokoto, Kebbi da Zamfara da €5m

Masu bukata ta musamman daga jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi zasu samu tallafin €5m daga turawan mishan.

Gwamnatin Jamus ce zata ba da tallafin karkashin wata kungiya mai suna Christian Blind Mission.

Da yake yiwa kamfanin dillanci labarai na kasa karin bayani ranar larabar a Abuja, shugaban kungiyar, Dr Rainer Brokchaus yace shirin zai dauki tsawon shekaru 5 ana gudanar da shi domin karfafar wadanda rikici ya shafa a shiyyar Arewa maso Yamma.

Shirin zai fi mai da hankali kan yara da mata da kuma masu bukata ta musamman da nufin farfado da rayuwarasu.

A shekarun nan yankin arewa maso yamma ya zama wanda yafi jan hankalin kungiyoyi da masu bada agaji saboda yadda rikicin “Yan bindiga da ayyukan masu garkuwa da mutane ya daidaita shi.

Samuel Omoi, shi ne shugaban kungiyar a Najeriya, ya ce aikin zai rage radadin matsin da ake ciki a wadannan yankuna.

Nike Abimbola, Shugabar Shirye-shiryen a hukumar kula da masu bukata ta musamman (NCPWD), ta yaba wa wannan yunkurin, tana mai cewa zai magance matsalolin da mutanen da ke da nakasa ke fuskanta.

Turawa za su taimakawa mazauna Sokoto, Kebbi da Zamfara da €5m

Nigerian Govt moves to standardise national addressing system

Nigerian Govt confirms sack of workers with Benin Republic, Togo degrees