in

Yahaya Bello : Najeriya aljannar barayi – Sowore

Dan siyasa mai rajin kare hakkin dan Adam, Omoyele Sowore, ya bayyana Najeriya a matsayin “aljanna ga masu satar dukiyar kasa.”

Sowore ya yi wannan tsokaci ne bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da. A tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello beli.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin Bello a kan kudi Naira miliyan 500 tare da bukatar a samu mutane biyu da za su tsaya masa.

Bello ya musanta tuhume-tuhume 19 da EFCC ta gabatar a kansa.

Ana zargin Bello da aikata almundahanar kudin har Naira biliyan 80.

A zaman kotun da aka yi a ranar Juma’a, Mai shari’a Nwite ya bayar da belin tsohon gwamnan bisa sharadin biyan Naira miliyan 500.

A martaninsa, Sowore ya koka da cewa Bello ya zama wani gwarzo a cikin dakin kotun bayan da alkalin ya bayar da belinsa.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce:

“An ba Yahaya Bello beli, nan take ya zama gwarzo a cikin dakin kotu! Abin da kawai za ka yi shi ne ka sace isasshen kudin da zai talauta talakawa kuma ya kara wa masu hannu da shuni arziki; daga nan sai ka zama gwarzon talakawa da masu kudi. Najeriya aljanna ce ga masu sata.”

Yahaya Bello : Najeriya aljannar barayi – Sowore

EPL: Iwobi credits Fulham manager for impressive form

Nigeria cannot achieve meaningful development without power sector reforms –VP Shettima