Rundunar ‘yan tawaye karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham ta samu nasarar kawo karshen mulkin shugaba Bashar Al asad na shekaru 24.
A safiyar yau Lahadi suka bayyana karbe iko da babban birnin kasar, Damascus, da kuma hambarar da Shugaba Bashar al-Assad.
Kawo yanzu ba a san inda Mr al-Assad yake ba, amma ‘yan tawaye sun ce ya tsere daga kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu majiyoyin soji biyu da ke tabbatar da cewa jirgin shugaban ya fice daga Siriya zuwa wata kasa da ba a bayyana ba.
DAILY POST ta ruwaito cewa rundunar ‘yan tawaye karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham ta samu manyan nasarori a kwanakin baya, inda ta karbe manyan birane kamar Aleppo da Homs.
A safiyar Lahadi, kwamandan HTS, Abu Mohammed al-Julani, ya ce za a ci gaba da kula da hukumomin gwamnati karkashin Firayim Ministan Mr al-Assad, Mohammad al-Jalali, har zuwa lokacin da za a mika ragamar mulki ga farar hula.
A ranar Asabar, zababben Shugaban Amurka, Donald Trump, a cikin wani sakon sa a X, ya yi murna da faduwar gwamnatin Mr al-Assad, amma ya ce Amurka ba za ta shiga cikin rikicin ba.
Ana ganin faduwar gwamnatin Mr al-Assad babban rauni ne ga Iran da Rasha, wadanda suka bai wa gwamnatinsa goyon baya sosai, ta hanyar aika makamai da ma’aikata domin yaki tare da sojojin Siriya kan ‘yan tawaye.
‘Yan adawar Siriya sun sanar da hambarar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad