Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da tsohon dan majalisar wakilai Dokta Joseph Haruna Kigbu a yammacin jiya Litinin a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jos.
Harin ya faru da misalin karfe 6:00 na yamma, a tsakanin hanyar Nunku da ke karamar hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa, da Gwantu a karamar hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
Yan bindigar sun harbe dansandan da yake tsaron Dr. Kigbu har lahira garin kokarin kubutar dashi daga harin.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi harbin kan mai uwa da wabi lamarin da ya firgita masu ababen hawa a yankin.
Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa batace komai ba game da lamarin.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar wakilai