Hukumomin tsaron kasar nan sun ce kimanin mayakan kungiyar Boko Haram dubu 130 ne suka ajiye makamansu a cikin watanni biyar da suka gabata a kasar.
Hafsan hafososhin kasar, Janar Christopher Musa shi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro kan al’amuran tsaro da ya halarta a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Alhamis.
Janar Christopher Musa ya ce a tsakanin ranar 10 ga wata watan Yuli zuwa 9 ga watan nan na Disamba, mayakan Boko Haram dubu 30 da 429 da mata dubu 36 da 774 da kuma yara dubu 62 da 265 su ne suka mika wuya.
An gudanar da taron na Qatar don yin nazari kan halin tsaro musamman na kasashen Afirka.
Yan Boko Haram 130,00 ne suka mika wuya a watanni biyar – Christopher Musa