Kimanin ƴan Najeriya dubu 3 da 270 sun samu takardun zama ƴan Amurka sakamakon shiga aikin sojin ƙasar a baya-bayan nan.
Najeriya ce ta huɗu a jerin ƴan ƙasashen da Amurka ta ba su takardun zama ƴan ƙasa ta hanyar hidinmta mata a ɓangaren aikin soji tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024.
A jumulce, Amurka ta bai wa ƴan ƙasashen ƙetare kimanin dubu 52 takardun zama ƴan ƙasa a ƙarkashin aikinsu na soji a ƙasar.
Alkaluman da hukumar kula da takardun Ƴan Ƙasa da Shige da Fice ta Amurka ta fitar a wannan Litinin, sun nuna cewa, ƴan asalin ƙasar Philippines dubu 5 da 630 ne suka samu takardun zama ƴan Amurka a ƙarƙashin aikin sojin, sai Jamaica da ke biye mata a matsayi na biyu, inda take da dubu 5 da 420, yayin da Mexico ke a matsayi na uku, inda take da dubu 3 da 670. Sai kuma Najeriya da ta zo ta biyar da adadin mutum dubu 3 da 270 da suka shiga aikin sojin tare da samun takardun zama ƴan Amurka.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Ghana da Haiti da China da Kamaru da Vietnam da Koriya ta Kudu kamar yadda alkaluman hukumomin Amurka suka nuna.
Alkaluman sun nuna cewa, adadin ƴan Najeriya da ke shiga aikin soji a Amurka na ci gaba da karuwa a kai a kai cikin shekaru biyar da suka gabata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗimbin matasan kasarnan ke fafutukar neman shiga aikin soji a ƙasar nan, amma abin ya ci tura, yayin da ake zargin cewa, ƴan siyasa sun yi babakere wajen mamaye guraben da ake da su.
‘Yan Najeriya 3,270 sun samu takardun zaman ‘yan Amurka sanadiyar shiga aikin soji