in

‘Yan Sanda sun dakile Yunkurin Garkuwa da Mutane Biyu, kuma Sun Ceto Mutane 20 a jihar Katsina

‘Yan Sanda sun dakile Yunkurin Garkuwa da Mutane Biyu, kuma Sun Ceto Mutane 20 a Jihar Katsina

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Katsina ta dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a wurare biyu daban-daban a Kananan Hukumomin Jibia da Faskari, tare da ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, ASP Abubakar Sadiq, ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi cewa, lamarin farko ya faru ne a ranar 7 ga Disamba, 2024, da misalin karfe 7:00 na yamma, a Kwanar Makera, kan hanyar Katsina–Magamar Jibia, cikin karamar hukumar Jibia.

Ya ce wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai irin su bindigogi kirar AK-47 sun bude wuta kan wata mota da ke tafiya, suna kokarin sace mutanen da ke cikinta.

“Amma jami’an rundunar da aka tura daga ofishin Rundunar ‘Yan Sandan Jibia, bisa samun bayanan sirri, sun gaggauta zuwa wurin tare da fafatawa da ‘yan bindigar a inda suka tilasta musu tserewa daga wurin da raunukan harbin bindiga. Dukkan mutane goma da ke cikin motar an ceto su ba tare da ko daya ya ji rauni ba.” inji kakakin rundunar

A wani lamari makamancin haka, a kiya Asabar da misalin karfe 8:30 na dare, a Marabar Bangori, kan hanyar Funtua–Gusau a Karamar Hukumar Faskari, wasu ‘yan bindiga sun yi kwantan bauna kan wata mota dauke da fasinjoji.

Jami’an ‘yan sanda, bayan samun bayanai kan lamarin, sun hanzarta zuwa wurin tare da fuskantar ‘yan bindigar, nana ma dai sun tsere ba tare da samun damar aiwatar da shirinsu ba

DAILY POST ta ruwaito kwamishinan ‘yan sandan Jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya jinjinawa jajircewar jami’an da kwarewar su a yayin aikin, tare da ba su kwarin gwiwar ci gaba da tsayawa daram domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.

‘Yan Sanda sun dakile Yunkurin Garkuwa da Mutane Biyu, kuma Sun Ceto Mutane 20 a jihar Katsina

Plateau FA organises inter-security agency football tournament

EPL: We’re not favourites – Maresca speaks ahead of Tottenham vs Chelsea clash