Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta Lukarawa za ta zama “tarihi nan ba da jimawa ba.”
Laftanal Janar Oluyede ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da Shugaban Bola Tinubu ranar Litinin a Abuja.
“Muna kai musu farmaki mai tsanani a bangaren Najeriya, kuma da zarar mun kai musu hari sosai nan, suna tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.
“Yanzu da Jamhuriyar Nijar ta fara shiga cikin wannan aiki, hakan na nufin nan ba da jimawa ba, kungiyar Lukarawa za ta zama tarihi,” in ji shi.
Oluyede ya jaddada muhimmancin haɗin kai da ƙasashen makwabta don magance barazanar kungiyar da ke tsallake iyakoki.
A ranar Litinin, 9 ga watan Disamba ne Laftanal Janar Oluyede ya shiga ofis a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya.
Yan ta’addan Lakurawa za su zama tarihi – Laftanal Janar Oluyede