in

Yan wasan Kano Pillars 3 zasu bugawa Najeriya wasa

Mai horar da tawagar Super Eagles B Augustine Eguavoen, ya gayyaci yan wasa 30, don bugawa Najeriya wasa da kasar Ghana a wasan share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika ta yan wasan cikin gida.

Gasar wadda itace karo na 8 zata gudana daga farkon watan Fabrairun 2025 a kasashen Kenya, Uganda da kuma Tanzania.

Tuni yan wasa 30 irinsu Rabiu Ali, na Kano Pillars da ya ci kwallo 8 a kakar bana, da yan wasa irinsu Musa Zayyad na Elkanemi da na Rivers United Steven Mayo suka samu goran gayyata don buga wasan.

Du ka yan wasan da aka gayyata zasu isa sansanin kungiyar Remo Stars da ke Ikenne na jihar Ogun a yau Laraba 4 ga Disamba shekarar da muke ciki.

Ana saran wasan farko da Super Mario B za suyi da tawagar Ghana zai gudana a filin wasa na Accra Sports Stadium a ranar 22 ga Disambar da muke ciki.

Sai kuma wasa na biyu da zai gudana a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo a ranar Asabar 28 ga Disambar shekara da muke ciki.

Jumullar yan wasa 30 da aka gayyata domin isa sansanin tawagar Super Eagles B sun hada da masu tsaran raga Henry Ozoemena (Enyimba FC); Kayode Bankole (Remo Stars); Nurudeen Badmus (Kwara United)

Yan wasan baya kuwa Ismail Sadiq (Remo Stars); Waliu Ojewole (Ikorodu City); Imo Obot (Enyimba FC); Taiwo Abdulrafiu (Rivers United); Junior Nduka (Remo Stars); Victor Collins (Nasarawa United); Ifeanyi Onyebuchi (Rangers International); Steven Mayo (Rivers United)

Yan wasan tsakiya sun hada da Jide Fatokun (Remo Stars); Rabiu Ali (Kano Pillars); Saviour Isaac (Rangers International); Musa Zayyad (El-Kanemi Warriors); Emmanuel Ogbole (Kwara United); Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes); Kazeem Ogunleye (Rangers International)

Yan wasan gaba kuwa akwai Anas Yusuf (Nasarawa United); Adamu Abubakar (Plateau United); Osy Martins (Lobi Stars); Sikiru Alimi (Remo Stars); Temitope Vincent (Plateau United)

Sauran sune Samuel Ogunleye (3SC); Abiam Nelson (Kano Pillars); Meyiwa Oritseweyimi (Bendel Insurance); Ngbemena Ikechukwu (Heartland FC); Sunday Megwo (Abia Warriors); Umar Al-Amin Ibrahim (El-Kanemi Warriors); Adams Aminu Sani (Kano Pillars)

Yan wasan Kano Pillars 3 zasu bugawa Najeriya wasa

Hookup responsible for high rate of missing girls – Police

CBN ya umarci bankuna su cika na’urar ATM da kudi