in

Za a yi hazo da kura a Najeriya daga Juma’a zuwa Lahadi – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta Yi Hasashen Hazo da kura a fadin kasar nam daga Juma’a zuwa Lahadi

NiMet ta bayyana haka ne inda ta ce za a sami hazo da kura a sassa daban-daban na kasar.

A sanarwar da aka fitar a Abuja ranar Alhamis, NiMet ta ce ana sa ran hazo mai matsakaiciyar kura a yankin Arewa a ranar Juma’a, daga tsawon kilomita 2 zuwa 5.

“A Jihohin arewa ta tsakiya ana sa ran za su fuskanci hazo mai dan karfi, yayin da yankin Kudu zai sami hazo mai matsakaiciyar Kura.

A ranar Asabar, NiMet tayi hasashen hazo mai sosai a yankin Arewa, tare da kira da zai rage hangen nesa daga kilomita 2 zuwa 5,

“A yankin Kudu, ana sa ran samun hazo mai dan karfi a duk tsawon lokacin.”

A ranar Lahadi kuma, NiMet ta yi hasashen hazo mai matsakaiciyar kura tare rage hangen nesa daga kilomita 2 zuwa 5 a yankunan Arewa ta tsakiya.

NiMet ta gargadi jama’a su dauki matakan kariya saboda hazo na dauke da kura a cikin iska, wanda ka iya cutar da masu matsalar numfashi, musamman wadanda ke fama da asma.

Hukumar ta kuma bukaci masu amfani da jiragen sama su tuntubi rahotannin yanayi na tashoshin jiragen sama domin tsara tafiye tafiyensu yadda ya dace.

Za a yi hazo da kura a Najeriya daga Juma’a zuwa Lahadi – NIMET

Customs: Oyo-Osun Area Command generates N72bn in 11 months

Northern senators visit Buhari in Daura