Hukumar shirya gasar League din kasar Amurka, ta sanar da ranar fara gasar MLS ta kakar wasannin shekarar 2025/2026.
Gasar wadda ake sa ran farawa a ranar 22 ga Fabrairun shekara mai kamawa, da akalla kungiyoyi 30 zasu kece raini da junansu.
Kungiyar da Lionel Messi ke jagoranta Inter Miami FC, ce zata fara bude wasan farko da NYCFC a birnin Fort Lauderdale da ke kasar ta Amurka.
Gasar ta MLS dai za a fafata wasanni 34, wato ko wacce kungiya zata buga wasa 17 a gida da kuma 17 a waje.
Hakazalika, gasar ta shekara mai kamawa zata kunshi sabbin kungiyoyi kamar su San Diego FC, DC United.
Za’a fara gasar MLS ta Amurka a Fabrairun 2025