in

Za’a fara hukunta wadanda suke shigar da korafen gaibu akan masu shari’a – CJN

Babbar Jojin kasa, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa bangaren shari’a na binciken hanyoyin da za a bi wajen hukunta duk wanda yayiwa wani alkali kazafi domin dakile yawan korafe korafen gaibu da ake shigarwa barkatai.

Mai shari’a Kekere-Ekun ta ce majalisar shari’a ta kasa (NJC) za ta binciki korafe-korafe na gaskiya a kan jami’an shari’a yayin da kuma za ta tallafa wa alkalan da akayiwa kazafi don tabbatar da anyi musu adalci.

Ta bayyana hakan yayin da take jawabi a wajen bude taron shekara-shekara na alkalan kotun daukaka kara a ranar Litinin a Abuja.

Mai shari’ar ta sake jaddada aniyar majalisar na sauya mumman kallon da wasu ke yiwa bangaren shari’a a tsakanin al’umma.

Ta shawarci shugabannin kotuna da su rika gudanar da tarukan bita akai-akai don kaucewa yanke hukunci masu karo da juna da kuma bin diddigin hukunce-hukuncen kotunan shari’a da dalilan yanke hukunci.

Za’a fara hukunta wadanda suke shigar da korafen gaibu akan masu shari’a – CJN

BREAKING: Yahaya Bello loses as court strikes out bail application

Alleged defamation: Court to hear case between Farotimi, Afe Babalola