in

Zamfara ba zata taɓa yin sulhu da ‘Yan bindiga ba

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta taɓa la’akari da yin sulhu da ‘yan bindiga ba.

Ya bayyana cewa, gwamnatin Jihar Zamfara ba ta cikin wani gaggawa na cimma wata yarjejeniya da ‘yan bindiga ba.

Ya bayyana wannan ne a lokacin wata hira a shirin Politics Today na Channels Television

“Ai na bayyana matsayina a kan batun sulhu da ‘yan bindiga tun daga farko.

“Ba na cikin wani gaggawa na yin sulhu da waɗannan mutanen. Ba zan taɓa yin sulhu da kowanne ɗan bindiga ba. Wannan shi ne matsayina tun da farko. Ina ganin ana iya yin sulhu ne a lokacin ƙarfi, ba a lokacin rauni ba,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da ‘yan sanda, sojoji, da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a jihar.

Zamfara ba zata taɓa yin sulhu da ‘Yan bindiga ba

Babajimi Benson ya nemi karin kudi ga hukumar binciken tsaro ta kasa

Senate orders reinstatement of sacked NRC worker, payment of entitlements