in

Zanga-Zangar tsofaffin sojoji kan rashin biyan fansho ya isar da mummunan sako – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani, ya nuna damuwarsa game da zanga-zangar da tsofaffin sojoji suka yi kan rashin biyan fansho da sauran hakkokin da ake binsu.

Sani ya ce wannan lamari na aika da sako mara kyau ga wadanda ke cikin ayyukan soja da kuma waɗanda ke kan gaban yaki, suna sadaukar da rayukansu don tsaron kasar da zaman lafiya.

DAILY POST Hausa, ya ruwaito cewa, tsofaffin sojoji sun gudanar da zanga-zanga a cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja, kan rashin biyan fansho da sauran hakkokinsu.

A yayin da yake tsokaci game da lamarin, Sani, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya koka da cewa mutanen da suka sadaukar da rayukansu ga al’umma a yanzu su ne suke daga takardu domin neman biyan fanshonsu.

Ya ce: “Zanga-Zanga da tsofaffin ma’aikata suka yi a Abuja kan rashin biyansu fansho yana aika da mummunar sigina ga wadanda ke aiki da kuma Wanda suke fagen daga suna sadaukar da rayuwarsu domin tsaro da zaman lafiyar kasarmu. Ta yaya mutanen da suka sadaukar da rayukansu domin mu yanzu zasu na daga takardu domin neman biyan fanshonsu.”

Zanga-Zangar tsofaffin sojoji kan rashin biyan fansho ya isar da mummunan sako – Shehu Sani

International Anti-corruption Day: EFCC urges youths to pursue values, shun crime

Court okays hearing of N5.2bn suit against Chinese over alleged false claims